Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Bayern Munich ta lashe Bundesliga, Barca da Real sun yi bukin jefa kwallaye 5 a raga

Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga karo na 23 bayan ta doke Frankfurt ci 1-0 a ranar Assabar, A bana kuma Bayern Munich ta lashe kofin ne da tazarar maki 20 tsakaninta da Borussia Dortmund wacce ta lashe kofin a jere shekaru biyu da suka gabata.

'Yan wasan Bayern Munich sun daga kocinsu sama a lokacin da suke murnar lashe kofin Bundesliga a karshen mako
'Yan wasan Bayern Munich sun daga kocinsu sama a lokacin da suke murnar lashe kofin Bundesliga a karshen mako REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Yanzu haka kuma saura wasanni shida a kammala dukkann wasannin na Bundesliga a bana.

Bayan lashe kofin Bundesliga, Bayern Munich tana neman yin guzurin kofuna uku ne a bana da suka hada da kofin kasar Jamus da kuma kofin gasar Zakarun Turai inda za ta sake kece raini da Juventus a zagayen kwata Fainal.

Spain

Real Madrid da Bercelona sun yi bukin jefa kwallaye 5 a karshen mako inda a karon farko Cesc Fabregas ya jefa kwallaye uku a raga tun daworsa Barcelona daga Arsenal wanda ya taimakawa Barcelona lallasa Real Mallorca ci 5-0 wasan da kuma aka buga ba tare da Lionel Messi ba.

Gonzalo Higuain, da Kaka da Cristiano Ronaldo da Mesut Ozil su ne ‘Yan wasan da suka jefawa Real Madrid kwallayenta biyar a ragar Lavente.

Yanzu dai wasanni 9 suka rage a kammala La liga kuma tazarar maki 13 ne Barcelona taba Real Madrid a teburin gasar.

Faransa

St Etienne ta hauro matsayi na uku a teburin League 1, amma Lyon ta sha kashi ne ci 1-0 a hannun Reims.

A ranar Assabar ne, Paris St Germain ta samu nasarar ci gaba da jagorancin teburin gasar da maki 7 tsakaninta da Marseille bayan ta doke Rennes ci 2-0.

Italiya

A Seria A, Fiorentina ta rike AC Milan ci 2-2, Wasa kuma bai yi wa Inter Milan dadi ba domin cikin mintina 12 ne Denis dan wasan Atlanta ya rama kwallaye uku da ya sa aka tashi wasa ci 4-3 bayan Inter ta fara jefa kwallaye uku a raga.

Juventus kuma ta doke Pescara ne ci 2-1 kuma Juve ce ke jagorancin teburin gasar da maki 71 sai Napoli da ke bi mata da maki 62.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.