Isa ga babban shafi
FIFA

Mourinho ya zargi FIFA da yin coge a zaben gwarzon kocin Duniya

Jose Mourinho na Real Madrid ya zargi Hukumar FIFA da yin magudi wajen zaben gwarzon kocin Duniya, yana mai cewa an karkatar da kuri’un wadanda suka zabe shi ne zuwa ga kocin Spain Vicente del Bosque.

José Mourinho, Kocin Real Madrid a Spain
José Mourinho, Kocin Real Madrid a Spain Reuters
Talla

Mourinho shi ne ya zo a matsayi na biyu daga kuri’un ‘Yan jaridu da masu horar da ‘yan wasa suka kada.

Kocin na Real Madrid ya ce ya san za’a yi magudi a zaben, shi ya sanya ya kaucewa zaman taron a birnin Zurich a watan Janairu.

Mourinho ya shaidawa wata kafar Telebiin din kasar Portugal cewa wadanda suka kada kuri’ar zaben da dama sun kira shi tare da tabbatar ma shi da cewa shi ne suka zaba amma kuma ba zabinsu ba ne FIFA ta bayar. Inji shi Mourinho.

Sai dai FIFA ta tabbatar da gaskiyar zaben tare da wallafa wakilan da suka jefa kuri’a.

Kazalika Mourinho ya kalubalanci kyautar zakaran gwarzon dan wasan Duniya da aka ba Lionel Messi karo na hudu, yana mai cewa Cristiano Ronaldo ne ya cancanci a ba shi kyautar domin shi ne ya lashe kofin La liga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.