Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kunya ta hana wa Pistorius fitowa horo

Dangin Oscar Pistorius, dan tseren gudun nakkasassu na kasar Afrika ta kudu sun ce kunya ta hana dan wasan fitowa yin horo bayan an tuhume shi da kisan budurwar shi a ranar valentine 14 ga watan fabraru.

Oscar Pistorius a lokacin da ya gurfana a gaban kotu
Oscar Pistorius a lokacin da ya gurfana a gaban kotu REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A makon jiya ne Pistorius ya samu sassauci daga kotu inda aka ba shi damar yin tafiye tafiye domin shiga wasanni a wasu kasashen duniya, amma kawun shi Arnold Pistorius yace ai dan wasan yana cike da kunya da har ya kasa fita a cikin gida.

Kawun nasa yace sai dai anan gaba, Dan wasa ya fito horo amma ba yanzu ba.

Tauraruwar dan wasan dai ta dushe ne tun mutuwar budurwar shi Reeva Steenkamp a Valentine's Day.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.