Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Manchester ta doke Shenhua, Liverpool da Chelsea sun sha kashi

Kungiyar Manchester United ta Ingila ta doke kungiyar Shanghai Shenhua ta China ci 1-0 a wasannin share fagen wasannin kaka wasa, kuma Kagawa ne ya zirawa Manchester kwallonta a raga ana minti 68 da fara wasa.

Shinji Kagawa dan wasan Manchester United kusa da 'Yan wasan Shanghai Shenhua bayan ya zira kwallo a raga.
Shinji Kagawa dan wasan Manchester United kusa da 'Yan wasan Shanghai Shenhua bayan ya zira kwallo a raga. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Liverpool kuma ta sha kashi hannun Roma ci 2-1, wasan Farko da Brendan Rodgers ya sha kashi a matsayin Koci.

Kazalika, kungiyar Chelsea ta sha kashi a Amurka hannun Major League All Stars ci 3-2. Duk da John Terry and Frank Lampard ne suka zirawa Chelsea kwallayenta a raga ana ci 2-1 kafin daga bisani All Stars su barke kwallayen.

A tawagar Major League All Stars akwai David Beckham da Thierry Henry amma Chris Wondolowski da Chris Pontius da Eddie Johnson ne suka zira kwallaye a raga.

kungiyar Chelsea ta sha kashi ne a dai dai lokacin da ta ke kammala cinikin dan wasan Brazil Oscar daga Internacional akan kudi sama da Dala Miliyan 38.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.