Isa ga babban shafi

Macron ya kaddamar da bikin baje kolin kayan noma a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kaddamar da wani shirin baje kolin harkokin noma a kasar wanda aka saba yi shekara shekara, a yayin da manoma suka yi Shewa suna bushe bushen  usur da ke nuni da ba sa marabtar yanayin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS - HANNIBAL HANSCHKE
Talla

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun nisanta masu zanga-zangar daga inda shugaban yake yayin da ya ke rangadin bikin baje kolin, inda ya dandana wasu daga cikin kayayyakin da aka gabatar a wurin baje kolin.

Sai dai yayin da ya shiga wurin, daruruwan masu zanga-zangar sun yi arangama da 'yan sanda a yayin da suke kokarin samar da hanya ga shugaban.

Daga bisani dai an rufe kasuwar baje kolin saboda yadda wasu suka ta da hankali, amma aka sake bude wa domin jama'a su ci gaba da kai komonsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.