Isa ga babban shafi

Birtaniya da Japan sun fada cikin matsin tattalin arziki

Tattalin arzikin Birtaniya ya fada cikin mawuyacin hali na matsi, a yayin da Japan ta bi sahu, lamarin da ya sa yanzu Jamus ta zama kasa ta 3 mafi karfin tattalin arziki a duniya  a halin da ake ciki.

Fira Ministan Ingila,  Rishi Sunak.
Fira Ministan Ingila, Rishi Sunak. via REUTERS - ©UK Parliament/JESSICA TAYLOR
Talla

A wannan rana ta Alhamis ce alkalumma na hukuma suka nuna cewa tattalin arzikin Birtaniya ya shiga garari a karshen shekarar 2023, lamarin da ya yi mummunan tasiri ga yunkurin Fira Minista Rishi Sunak na bunkasa tattalin arziki.

Kasar ta samu koma baya na tattalin arziki da kashi 0.3 a watanni uku na karshen shekarar 2023, idan aka kwatanta da watanni uku da suka gabaci lokacin, biyo bayan tabarbarewa na kashi 0.1 a rubu’i na uku, kamar yadda alkalumman da ofishin kididdigar kasar ya wallafa ya nuna.

Rubu’i biyu a jere ne tattalin arzikin Birtaniya ya samu koma baya,  abin da  ake dauka a matsayin matsin tattalin arziki, kodayake wasu masana sun bayyana  hakan a  matsayin tsaiko.

Ita ma Japan ta bi wannan sahu na faduwar tattalin arziki, indat a sauka daga matsayi na 3 a duniya, a yayin da Jamus ta maye gurbinta, biyo bayan habaka ta kashi 5 da digo 7 da tatttalin arzikinta ya yi a shekarar 2023.

Jamus ta dare wannan matsayi ne sakamakon ci gaban da tattalin arzikinta ya samu da sama da kashi 6 a cikin karshen shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.