Isa ga babban shafi

Sabon Firaministan Faransa Gabriel Attal ya kafa majalisar ministocinsa

Sabon Firaministan Faransa Gabriel Attal mai shekaru 34 a duniya, ya wallafa jerin sunayen mutanen da za su aiki da shi a matsayin ministoci cikin gwamnatinsa, bayan da ya samu sahalewar shugaban kasar Emmanuel Macron. 

Zaman farko da Firaminista ya yi da jerin mutanen da ya bai wa mukaman ministoci a Ofishinsa.
Zaman farko da Firaminista ya yi da jerin mutanen da ya bai wa mukaman ministoci a Ofishinsa. © via Reuters
Talla

A cikin sabuwar majalisar ministocin, Gabriel Attal ya tabbatar da wasu makusantan Emmanuel Macron a kan mukamansu, yayinda ya dawo da wasu fitattun mutane da suka hada da ministan cikin gida Gerald Darmanin da ministan kudi Bruno Le Maire, sai kuma na tsaro Sebastien Lecornu. 

To sai dai ita ministar harkokin wajen Catherine Colonna ta rasa mukaminta domin kuwa tuni Attal ya damka shi a hannun sakataren jam’iyyar Macron wato Stephane Sejourne mai shekaru 38 a duniya. 

Stephane dai ya kasance daya daga cikin gungun ‘yan majalisar dokoki da ke kare manufofin kungiyar Turai, yayin da a hannu daya ya kasance daga cikin ‘yan siyasar Faransa na farko-farko da suka fito fili karara domin nuna cewa suna rayuwa ce irin ta masu auren jinsi, sannan kuma ba wani ba ne abokin zaman face sabon firaminista Gabriel Attal. 

Kafa sabuwar gwamnatin dai ya biyo bayan murabus din da Elysabeth Borne ta yi daga mukamin Firaminista a farkon wannan mako ne, bayan share watanni kusan 20 a kan wannan matsayi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.