Isa ga babban shafi
YAKIN ISRA'ILA DA HAMAS

Kamfanin jiragen ruwan Faransa ya koma anfani da mashigar tekun Bahar Maliya

Katafaren kamfanin jiragen ruwa na kasar Faransa CMA-CGM ya ce zai ci gaba da amfani da hanyar tekun Bahar Maliya, kwanaki bayan da kamfanin Maersk na kasar Denmark ya sanar da cewa zai dawo amfani da wannan hanya, yayin da rundunar hadaka ta sojojin ruwa karkashin jagorancin Amurka ke aikin kula da hanyar saboda hare-haren 'yan tawayen Yemen.

Wani jirgin dakon kaya da mayakan Houthi suka kwace shi a tekun Bahar Maliya.
Wani jirgin dakon kaya da mayakan Houthi suka kwace shi a tekun Bahar Maliya. AP
Talla

Hare-haren sun sa kamfanonin sufurin jiragen ruwa sauya hanya zuwa yankin kudancin Afirka a farkon wannan watan abin da ya kasance tafiya mai tsawo da tsada fiye da hanyar Bahar Maliya da ke da alaka da mashigin Suez.

A makon da ya gabata ne Amurka ta kaddamar da wata rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa domin dakile hare-haren makami mai linzami da mayakan Huthi da ke kan hanyar, wadda ke daukar kashi 12 cikin 100 na kasuwancin duniya ke kai wa.

'Yan Huthi dai sun ce suna kai hari kan Isra'ila da jiragen ruwan da ke da alaka da Isra'ila domin ganin an dakatar da kai farmaki a zirin Gaza, inda Isra'ila ke fafatawa da mayakan Hamas.

Kamfanin na Faransa, a cikin sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa wasu jiragensa sun bi ta cikin tekun Bahar Maliya, saboda binciken da ya y ikan yadda ma’aikatansa za su yi amfani da wannan hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.