Isa ga babban shafi

Faransa za ta haramta zukar taba sigari a wuraren shakatawa da makarantu

Mahukuntan Faransa sun sanar da shirin haramta zukar taba sigari a wuraren shakatawa na bakin ruwa da sauran wuraren taruwar jama’a musamman wadanda ke gab da makarantu, a wani yunkurin na dakile matsalar rasa rayuka sanadiyyar dabi’ar ta zukar taba sigari.

WHO ta ce kamfanonin taba sigari ne kan gaba wajen gurbata muhalli.
WHO ta ce kamfanonin taba sigari ne kan gaba wajen gurbata muhalli. AP - FRANCOIS MORI
Talla

Rahotanni sun ce a duk shekara ana samun mace-mace dubu 75 masu alaka da taba sigari a sassan Faransa, dalilin da ya tilasta mahukuntan kasar daukar wannan mataki.

Manufar wannan doka a cewar mahukuntan shi ne tseratar da yaran da ke tasowa daga ta'ammali da tabar wadda masana ke ci gaba da gargadi game da illarta ga lafiyar bil'adama.

Zuwa nan da shekarar 2032 ne Faransa ke fatar kammala tsaftace jama'arta daga ta'ammali da taba sigarin ta hanyar samar da yaran da za su taso daga yanzu zuwa wannan lokaci wadanda basa busa sigari.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta jima ta na zargin kamfanonin sigari da taka muhimmiyar rawa wajen gurbata muhalli baya ga haddasa asarar dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.