Isa ga babban shafi

Harin 'yan bindiga a Mexico ya kashe mutane kusan 30

Mahukunta a Mexico sun ce hare-haren ‘yan bindiga har biyu sun yi sanadin mutuwar mutane 24 cikin su, jami’an ‘yan sanda 12  a yanakuna kasar da ke fama da tashe-tashen hankula da ke da nasaba da  masu safarar muggan kwayoyi. 

Ana sanya ran adadin mamatan ka iya karuwa saboda yawan wadanda suka jikkata
Ana sanya ran adadin mamatan ka iya karuwa saboda yawan wadanda suka jikkata REUTERS - STRINGER
Talla

A jihar Guerrero da ke kudancin kasar, wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kai wa jami’an tsaro da ke sintiri  a Coyuca de Benitez, kamar yadda mai gabatar da kara, Alejandro Hernandez ya bayyana. 

Wannan harin ya rutsa da wani babban jami’in tsaron kasar da ke balaguro a cikin wani ayari, inda har masu tsaron lafiyarsa duk sun kwanta  dama. 

An kaddamar da bincike a game da musabbabin wannan mummunan hari.

A sakamakon farko-farko da jami’an tsaro suka fitar sun ce na gano mutane cikin mawuyacin hali a wajen da lamarin ya faru sakamakon bata kashin.

Bayanai sun ce hari na biyu da ‘yan bindigar suka kai yankin Michoacan na yammacin kasar ya kashe mutane 5 da wasu 2 da suka gamu da mummunan raunuka.

Haka kuma wasu gungun ‘yan bindigar sun farwa dan uwan mataimakin magajin garin Tamcambaro, kamar yadda mai gabatar da kara na kasar ya sanar.

Wani fai-fan bidiyo da aka rika yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ‘yan bindigar suka rika budewa jama’a wuta yayin da suke tserewa kan babura.

Kididdiga ta nuna cewa daga 2006 da ayyukan ‘yan bindiga suka yi kamari a kasar, mutane dubu 420 ne suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.