Isa ga babban shafi

Mutane 21 sun mutu bayan motarsu ta kama da wuta Italiya

Akalla mutane 21 sun rasa rayukansu da suka hada da kananan yara har ma da baki masu yawon bude ido bayan motarsu ta safa ta fado daga kan gada tare da kamawa da wuta a birnin Venice na Italiya.

Jami'an Agajin Gaggawa a kusa da motar da ta yi hatsari a Venice.
Jami'an Agajin Gaggawa a kusa da motar da ta yi hatsari a Venice. AFP - MARCO SABADIN
Talla

Akwai dimbin mutanen da suka jikkata a hatsarin na yammacin Talata, inda motar ta kife bayan ta fado daga kan gadar mai tazarar mita 10 zuwa kasa kamar yadda Kwamandan Jami’an Kashe Gobara ta Venice, Mauro Luongo ya shaida wa manema labarai.

Motar mai amfani da iskar gas na kan hanyarta ce ta dawowa daga Cibiyar Tarihi ta Venice da nufin mayar da  bakin sansaninsu, yayin da ta yi hatsari da misalin karfe 7:30 na yamma agogon GMT.

Bayanai na cewa, sauran fasinjojin da ke da sauran numfashi na cikin mawuyacin hali saboda munanen raunukan da suka samu.

Rahotanni na cewa, daga cikin wadanda suka mutun har da Faransawa da Jamusawa da kuma ‘yan asalin kasar Ukraine.

Jami’an Agajin Gaggawa sun kwashe tsawon sa’o’i a cikin dare suna aikin zakulo gawarwaki daga cikin motar ta safa.

Kawo yanzu babu wani bayani game da musabbabin aukuwar wannan mummunan hatsarin, amma an gano cewa, batirin motar ya kama da wuta, yayin da wasu ke cewa, rashin lafiya ta fuju’a ce ta kama direban motar, abin da ya sa tuki ya kufce masa.

Tuni shugabannin kasashen Turai suka fara aikewa da sakwannin ta’aziyarsu ga iyalalan mamatan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.