Isa ga babban shafi

Yankuna 50 daga cikin 96 na fuskantar tsananin zafi a Faransa

Miliyoyin mutane a Faransa na fuskantar barazanar tsananin zafi daga wannan Litinin zuwa nan da wasu ‘yan kwanaki, yanayin da kwararru suka yi gargadin cewa, baya ga tsanantar zafin zuwa sama da digiri 40, zai kara rura wutar dajin da ke addabar wasu yankunan kudu maso gabashin kasar.

Yadda jami'an kashe gobara ke kokarin kashe wutar dajin da tashi a dazukan yankin Cerbere da ke kudancin Faransa.
Yadda jami'an kashe gobara ke kokarin kashe wutar dajin da tashi a dazukan yankin Cerbere da ke kudancin Faransa. AP - Pierre Petit
Talla

Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa ana sa ran yanayin zafin da ake ciki ya kara tsananta a sassan kudancin Faransa a ranakun Talata da Larabar nan, yankunan da tuni yanayin zafin da suke fuskanta ya fara zarce makin digiri 40 a ma’aunin celcius.

Yadda tsanan zafi ya karar da wani karamin tafki a yankin gabashin Faransa.
Yadda tsanan zafi ya karar da wani karamin tafki a yankin gabashin Faransa. © Jeff Pachoud, AFP

A halin da ake ciki, mahukuntan Faransa sun ce, yankunan cikin kasar da suke fuskantar ibtila’in tsananin zafin sun karu zuwa 50 daga cikin 96, inda ake sa ran zafin ya tsananta daga makin digiri 40 zuwa 42, a yankin Rhone valley da ke yankin kudanci.

Kimanin jami’an kashe gobara 260 ne a yanzu haka suke fafutukar kashe wutar dajin da ta tashi a dazukan kauyen Chanousse da ke yankin kudancin na Faransa, inda tuni ta kone fadin kasar da ya zarce kadada 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.