Isa ga babban shafi

Wutar daji da fari sun addabi kasashen Turai

Jami’an kwana-kwana a Faransa na kokarin shawo kan gobara mafi muni da ta addabi kudancin kasar da wasu kasashen Turai a daidai lokacin da Birtaniya ta ayyana aukuwar fari a wasu sassan Ingila, a wani mataki da kungiyar EU ta kwatanta shekarar 2022 a matsayin mafi munin yanayin zafi da kudancin Turai ya taba fuskanta.

Jami'an kwana-kwana na ta kokarin kawar ad wutar dajin
Jami'an kwana-kwana na ta kokarin kawar ad wutar dajin AP - Noah Berger
Talla

Hukumar Kashe Gobarar ta Faransa ta ce ta gano bakin zaren wutar dajin da ta yi barna sosai a yankin kudu maso yammacin Faransa, amma ta bayyana cewa wannan rana ta Jumma’a ta kasance mai wahalar gaske ga ma’aikanta.

Da yake zanta wa da manema labarai mataimakin shugaban hukumar yankin Ronan Leaustic, ya ce wutar da ta mamaye tsawon kilomita 40 na sassan Gironde da Landes da ke kusa da Bordeaux ba ta ci gaba ba sosai a wannan Jumma’a, amma yanayin zafi da ya kai maki 37 a ma’aunin Celsius ya tilasta suyi taka tsantsan,".

Kimanin jami'an kashe gobarar Faransa 1,100 ke aikin, yayin da suka samu karin abokan aikinsu 361 daga kasashen Jamus da Poland da Ostiriya da Romania, tare da daukin jiragen feshin ruwa da dama daga rundunar Tarayyar Turai.

A wannan Juma’ar, ita Birtaniya ta ayyana samun fari a wasu sassan Ingila, mafi muni tun a shekarar 1935, biyo bayan karancin ruwan sama da aka samu na tsawon watanni da kuma yanayin zafi da ba a taba ganin irinsa ba a ‘yan makonnin nan.

Tuni hukumar da ke sa ido kan tauraron dan adam ta Tarayyar Turai ta sanar da cewa gobara da ta kona dubun-dubatar kadada na dazuzzukan kasashen Faransa da Spain da Portugal ta ayyana shekarar 2022 a matsayin mafi muni a yankin kudu maso yammacin Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.