Isa ga babban shafi

Covid-19 ta fara dawowa a kasashen Turai da Amurka

Hukumomin Kiwon Lafiya a Faransa sun lura da yadda ake samun karuwar masu ziyartar asibiti sakamakon rashin lafiyar da ke kama da cutar Covid-19 a daidai lokacin da sabon nau’in cutar ke yaduwa a kasashen Italiya da Birtaniya da kuma Amurka.

Sabon nau'in cutar Covid-19 da ake yi wa lakabi da Eris na yaduwa cikin gaggawa.
Sabon nau'in cutar Covid-19 da ake yi wa lakabi da Eris na yaduwa cikin gaggawa. via REUTERS - Social Media
Talla

Tun a karshen watan Yulin da ya gabata ne, cutar ta Covid-19 ta fara dawowa a Faransa dauke da wani sabon nau’in da aka yi masa lakabi da Eris ko kuma EG-5.

Har ila yau irin wannan nau’in na kan yaduwa a kasashen Italiya da Birtaniya da Amurka, yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce, tana kan sanya ido na kut-da-kut kan halin da ake ciki.

Hukumar Kula da Lafiyar Al’umma ta Faransa ta ce, alkaluman da aka tattara sun nuna cewa, an samu karuwar kashi 26 na adadin mutanen da ke zuwa sashen kulawar gagawa na asibiti, inda ake zargin cewa, cutar ta Covid-19 ce ke addabar su.

Masana kiwon lafiya a jami’ar Montpellier sun ce, nau’in Eris na yaduwa cikin gaggawa, sannan yana da karfin noke wa garkuwar jikin dan adam, yayin da yake kamanceceniya da nau’in Omicron wanda ake dauke da alamu na tari da zazzabi da mura.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.