Isa ga babban shafi

Mahammed Sala na Liverpool, ya ce sakaci ne ya hana su samun gurbi a gasar zakarun turai

Dan wasan gaban fagen kungiyar kwallon kafar Liverpool Mohamed Salah,  ya bayyana cewa, hankalinsa ya yi matukar tashi kan rasa gurbin buga gasar cin kofin Zakarun Turai a kaka mai zuwa. inda ya kara da cewa, babu wata magiya ko neman afuwa  da za a yi a kan wannan rashin nasara.

Mohamed Salah was kept in check as Liverpool suffered a first league defeat in 14 months
Mohamed Salah was kept in check as Liverpool suffered a first league defeat in 14 months AFP
Talla

Salah ya yi wannan sanarwa ne a shafin yada labaran  yanar gizo, jim kadan bayaan rashin nasarar da Liverpool ta cimma a bayan kungiyoyi hudun farko dake kan gaba,  sakamakon nasarar da Manchester United ta yi kan  Chelsea.

Liverpool da ta kare ne a matsayi na 5, za ta halarci gasar cin kofin kwallon kafar 'Europa League a kaka mai zuwa.

Dan kasar Masar mahamed  Sala, mai shekaru 30 a duniya ya bayyana cewa, sun kada magoya bayansu, haka kuma su da kansu.

Liverpool dai ta yi nasarar lashe wasanni bakwai daga cikin takwas da ta buga, a kokarinta na kaiwa ga matsayin na hudu, sai dai ba ta samu damar cimma wannan buri nata, bayan  buga wadannan  jerin wasanni da ta yi .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.