Isa ga babban shafi
Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Mohamed Salah ya ci gaba da nuna bajintar sa a Liverpool

Mohamed Salah ya ci gaba da nuna bajintar sa a Liverpool bayan da ya zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Atletico Madrid da ci 3-2 kuma ta dare saman rukunin B a gasar zakarun Turai.

Mohamed Salah ya ci kwallo biyu a wasan da Liverpool ta doke Atletico Madrid da ci 3 -2 a gasar zakarun Turai. 19/10/21.
Mohamed Salah ya ci kwallo biyu a wasan da Liverpool ta doke Atletico Madrid da ci 3 -2 a gasar zakarun Turai. 19/10/21. GABRIEL BOUYS AFP
Talla

Atletico ta yi rashin nasarar da ‘yan wasa goma a fili, bayan da aka kori Antoine Griezman a mintuna na 52 sakamakon yadda ya daga kafa fiye da kima har zuwa fuskar dan wasan Liverpool Roberto Firmino, bayan kwallaye biyu da ya zura a ragar Liverpool.

Sauran wasannin rukuni-rukuni na gasar Zakarun Turai da aka fafata ranar Talata.

Rukunin A

Bayaga wasan PSG da RB leipzig

Club Brugge -1 Manchester City- 5 

A rukunin B

Bayaga wasan Liverpool da Atletico Madrid

Fc Porto -1 Ac Milan- 0

A rukunin C

Besiktas -1 Sporting CP - 4

Ajax -4 Borussia Dortmund- 0

A rukunin D

Bayaga wasan Real da Shaktar Donetsk

Inter -3 Sheriff -1

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.