Isa ga babban shafi

An gudanar da bikin nadin Sarki Charles na III

Shugabannin Kasashen duniya da Sarakuna da kuma fitattun mutane sama da 2,300 suka halarci bikin nada Sarki Charles na III a matsayin wanda ya maye gurbin marigayiya Elizabeth ta biyu wadda ta rasu watanni 8 da suka gabata. 

Sarki Charles bayan an sanya masa kambin sarautar St Edward da bisa al'ada sau biyu kawai zai saka hular a lokacin mulkinsa.
Sarki Charles bayan an sanya masa kambin sarautar St Edward da bisa al'ada sau biyu kawai zai saka hular a lokacin mulkinsa. © AP - Victoria Jones
Talla

Da misalin karfe 12 na rana shugaban mabiya darikar Anglican, Archbishop Justin Welby ya dora hular zinare wadda ke zama hular mulki akan Sarki Charles a bikin da shi ne irinsa na farko tun bayan wanda aka yi a shekarar 1953. 

Nan da nan taron mutane 2,300 da suka halarci bikin su ka kaure da sowa inda suke fadin ‘God Save the King’, ‘Allah ya kare Sarki’ a gangamin da akayi a fadar Westminster Abbey, yayin da karar algaita ya mamaye wurin bayan kammala adu’o’in da aka yi na nadin sarautar.

Sarki Charles bayan an kammala daura masa kambin sarauta.
Sarki Charles bayan an kammala daura masa kambin sarauta. © AP/Aaron Chown

A wajen dakin taron kuwa, an yi ta harba bindigogi ne a fadin kasar da kuma akan teku, tare da kada kararrawa a mujami’un da ke birnin London.

Bisa al’ada, Sarki Charles mai shekaru 74 sau guda zai sanya hular sarautar St Edward a lokacin mulkinsa, yayin da aka nada uwargidansa Camilla mai shekaru 75 a matsayin mai rike da mukamin sarauniya a wani kwarya kwaryar bikin da aka yi. 

Kafin gudanar da bikin dai jami’an ‘yan sandan birnin London sun kama tarin masu zanga zanga wadanda ke adawa da masarautar da kuma korafi akan irin makudan kudaden da ake kashe mata. 

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun baje rubuce rubucen dake bayyana cewar, ‘wannan ba Sarkinmu bane’. 

Yayin da Yarima mai jiran gado William ke wucewa ciki masu zanga-zanga dauke da rubuce-rubucen nuna adawa da nadin mahaifinsa amatsayin sabon Sarki.
Yayin da Yarima mai jiran gado William ke wucewa ciki masu zanga-zanga dauke da rubuce-rubucen nuna adawa da nadin mahaifinsa amatsayin sabon Sarki. AP - Violeta Santos Moura

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tare da Amnesty International sun bayyana damuwa akan yadda jami’an tsaro suka yi ta kama masu adawa da bikin, yayin da HRW ta ce a birnin Moscow kawai ya dace aga irin wannan kame, amma ba London ba. 

Rundunar ‘yan sandan London ta baza jami’anta 11.500 a titunan birnin domin tabbatar da tsaro, yayin da ta gargadi duk masu shirya zanga zanga. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.