Isa ga babban shafi

Bazoum zai tallata Nijar a bukin rantsar da sarki Charles na 3 a Landan

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum na daga cikin shugabannin kasashen duniyar da aka gayyata Burtaniya domin halartar bikin nada Sarki Charles na III domin maye gurbin mahaifiyarsa Elizabeth ta II da ta rasu a ranar 8 ga watan Satumbar bara. 

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum na daga cikin shugabannin kasashen duniyar da aka gayyata Birtaniya domin halartar bikin nada Sarki Charles na III. 04/05/23
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum na daga cikin shugabannin kasashen duniyar da aka gayyata Birtaniya domin halartar bikin nada Sarki Charles na III. 04/05/23 © presidence du Niger
Talla

Bazoum na daga cikin shugabannin kasashen duniya da fitattun mutane 2000 da aka gayyata domin halartar bikin wanda za’ayi a ranar asabar mai zuwa, wanda shugaban mabiya darikar Anglican Archbishop na Canterbury, Justin Welby zai jagoranta watanni 8 bayan rasuwar Sarauniyar. 

Fadar gwamnatin Nijar tace shugaba Bazoum zai yi amfani da wannan dama wajen gudanar da wani taron kasuwanci da zuba jari a birnin London wanda ake saran manyan ‘yan kasuwa da masu zuba jari na kasashen duniya zasu halarta. 

Taron wanda aka yiwa suna ‘Destination Niger’ wani yunkuri ne na janyo hankalin masu zuba jari domin bada gudumawa wajen ci gaban kasar wadda ta samu habakar sama da kashi 12 a wannan shekara. 

Kasuwanci

Ana saran shugaban yayi amfani da wannan dama wajen yiwa bakin bayani akan harkokin kasuwanci da man fetur da ma’adinan karkashin kasa da kuma makamashin da Allah Ya wadata kasar da shi. 

Daga cikin tawagar shugaban akwai ministocin harkokin waje da kasuwanci da man fetur da kuma jakadiyar Nijar a Birtaniya. 

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen da Allah ya azirta su da ma’adinai iri-iri ciki harda uranium da man fetur da kuma zinare. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.