Isa ga babban shafi

Ganawar Ouattara da Bazoum kan rikicin kasahen yammacin Afirka

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya gana da Shugaban Cote D’ivoire Alassane Dramane Ouattara  yayin wata ziyara da ya kai birnin Abidjan da nufin lallubo hanyoyin takun saka dake da tsakanin kasashen Mali,Burkina Faso da Guinee da kungiyar Ecowas.

shugaba Mohamed Bazoum da Alassane Ouattara, kenan
shugaba Mohamed Bazoum da Alassane Ouattara, kenan AFP - SIA KAMBOU
Talla

A ranar 3 ga watan Yuli mai kamawa ne kasashen ECOWAS za su sake haduwa a birnin Accra na kasar Ghana domin sake  tattauna wa akan batun.

Dangane da Mali, muryoyi da dama ke fatan ganin an cirerwa kasar takunkumai, sai dai ana ci gaba da fuskantar tsaiko daga bangaren majalisar sojin kasar ta Mali, wacce ta kasa gabatar da jadawali na musamman dangane da batun zabe a wannan kasa.

zaben ne dai zai bayar da dama na sake mika mulki ga fararen hula, hakan ya sa mai shiga tsakani a rikicin na Mali, wato tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya kai wata ziyarar ba zata birnin Bamako, ba tare da ya bayar da wani karin bayani ga manema labarai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.