Isa ga babban shafi

Taron Shugabanin kungiyar ECOWAS ya watse baram-baram a Accra

Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma ko kuma ECOWAS sun gaza cimma matsaya a tsakanin su akan matakin da ya dace su dauka domin ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

Taron Shugabanin ECOWAS a Accra  na kasar Ghana
Taron Shugabanin ECOWAS a Accra na kasar Ghana © Rfi hausa
Talla

Bayan wani taro da shugabannin suka gudanar yau a Birnin Accra domin karbar rahotanni daga kwamitocin da suka kafa da kuma shawarwari, shugabannin sun yanke hukuncin dage taron nasu zuwa watan Yuli mai zuwa domin bada damar ci gaba da tintiba.

Wata majiya daga wurin taron tace bayan tafka mahawara, shugabannin sun kasa cimma matsaya akan matakin da ya dace a dauka akan kasar Mali, wadda taki gabatar da shirin mika mulki ga fararen hula da kuma katse hulda da kungiyar G5 Sahel dake yaki da ‘Yan ta’adda.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da matsayin kasar sa a wajen taron cewar, duk wani matakin ladabtarwar da za’a dauka akan sojojin a tabbatar da cewar ba zai yiwa jama’ar kasar illa ba.

Tuni kungiyar ECOWAS da AU suka sanar da dakatar da wadannan kasashe daga cikin su da kuma bukatar gabatar musu da shirin da sojojin ke da shi na mayar da mulki ga fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.