Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

Mali za ta tattauna da ECOWAS don mayar da kasar mulkin farar hula

Sojin da ke mulki a Mali sun sanar da fara tattaunawa da kungiyar ECOWAS da sauran kungiyoyi a kokarin cimma jituwa don mayar da kasar karkashin mulkin farar hula, matakin da ke zuwa bayan yawaitar takunkumai kan jagororin mulkin Sojin da kullewa kasar iyakarta da makwabta.

Jagoran mulkin Sojin Mali Assimi Goita.
Jagoran mulkin Sojin Mali Assimi Goita. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

A watan janairun da ya gabata ne ECOWAS ta dauki matakin dakatar da hada-hadar kasuwanci tsakaninta da Mali baya ga kulle iyakokin Malin da kasashen da ke makwabtaka da ita, lamarin da ya samu goyon bayan kasashen Faransa Amurka da kuma kungiyar Tarayyar Turai da dukkaninsu ke takun saka da kasar tun bayan juyin mulki.

Wannan mataki dai ya biyo bayan bukatar Sojin da ke mulki a Malin na neman ci gaba da kasancewa a madafun ikon a shekaru 5 masu zuwa gabanin mika mulki ga farar hula, duk kuwa da matsayar da aka cimma a baya na gudanar da zabe a ranar 27 ga watan Fabarairun da muke.

Sai dai a jiya laraba ma’aikatar da ke kula yankuna a Malin ta sanar da wani shirin sasantawa tsakaninta da ECOWAS da kungiyar tarayyar Afrika da kuma Majalisar Dinkin Duniya bisa jagoranci kasashen Mauritania da Senegal da kuma Ghana wadanda suka yi wata ganawa karon farko a ranar 31 ga watan janairu.

Sanarwar gwamnatin Sojin ta Mali ta ce aikin tawagar masu shiga tsakanin za ta yi kokarin samar da matsaya ta fuskar laluma tsakanin bangarorin bisa alkawarin komawar kasar karkashin mulkin farar hula.

A shekarar 2020 ne Soji suka kwace iko da Mali bayan tabarbarewar lamurran tsaro da durkushewar tattalin arziki da kuma rikicin kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.