Isa ga babban shafi

Jakadan ECOWAS ya isa Burkina Faso don tantance makomar dimokaradiyya

Mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS a Burkina Faso, Mahamadou Issoufou, ya isa birnin Ouagadougou domin tattaunawa da gwamnatin mulkin soja kan jadawalin komawa mulkin dimokaradiyya.

Shugaban gwamnatin Sojan Burkina Faso Lafatanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.
Shugaban gwamnatin Sojan Burkina Faso Lafatanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba. AFP - LEONARD BAZIE
Talla

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen na yammacin Afrika, ta dakatar da Burkina Faso, tare da yin barazanar daukar matakin ladabtarwa, matukar shugabannin kasar suka ki gaggauta sake mika mulki ga farar hula, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Janairu.

A farkon watan Yuni, ECOWAS ta nada Mahamdou Issoufou tsohon shugaban kasar Nijar a matsayin mai shiga tsakani a Burkina Faso, a maimakon laftawa kasar takunkumi wadda tuni ke fama da matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.

Ana sa ran Issofou ya gana da shugaban mulkin sojan Burkina Faso Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, da Firayim Minista Albert Ouedraogo da kakakin majalisar dokoki, Aboubacar Toguyeni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.