Isa ga babban shafi

ECOWAS ta aike da tan dubu 10 na kayan abinci ga Burkina Faso

Gwamnatin Burkina Faso ta ce kungiyar raya Tattalin Arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta aike da tan dubu 10 na kayan abinci ga kasar.

Tutar kungiyar ECOWAS a tsakiya wasu tutocin kasashe manbobinta.
Tutar kungiyar ECOWAS a tsakiya wasu tutocin kasashe manbobinta. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

Ministar harkokin wajen kasar Olivia Rouamba ta tabbatar da karbar tallafin a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.

A cikin watan Janairu, ECOWAS ta dakatar da gwamnatin da ke mulkin sojan Burkina Faso, biyo bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba Roch Marc Christien Kabore da sojojin suka yi, a karkashin jagorancin Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.

A ranar Litinin da ta gabata, gwamnatin sojin Burkina Faso ta ki amincewa da bukatar ECOWAS na neman rage wa’adin shekaru uku da ta dibarwa kanta kafin sake mikawa farar hula mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.