Isa ga babban shafi

Sojojin Burkina da Guinea sun nemi karin lokacin shirya zabe

Kungiyar kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, ta ce gwamnatocin mulkin sojan Burkina Faso da Guinea, sun bukaci karin lokaci domin gabatar da jadawalin mayar da mulki ga farar hula.

Shugaban kasar Burkina Faso laftanar Kanal Paul-Henri Damiba.
Shugaban kasar Burkina Faso laftanar Kanal Paul-Henri Damiba. © OLYMPIA DE MAISMONT/AFP
Talla

Kasashen biyu, sun gabatar da bukatar ce kwanaki biyu bayan cikar wa'adin da ECOWAS din ta basu dangane da tsara zabuka.

Bayan matakin dakatar da su daga cikinta da ta yi sakamakon juyin mulkin da sojojin kasashen na Guinea da Burkina Faso suka yi a karshen shekarar 2021 da kuma farkon 2022, a cikin watan Maris kungiyar ECOWAS ta bukaci gwamnatocin mulkin sojan su gabatar da jadawalin tsara zabukan maida wa farar hula mulki, ko kuma su fuskanci takunkumai, wa’adin da ya kare a ranar Litinin da ta gabata 25 ga watan Afrilu.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea Kanal Mamadi Doumbouya,a birnin Conakry, 10 ga Satumban, 2021.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea Kanal Mamadi Doumbouya,a birnin Conakry, 10 ga Satumban, 2021. REUTERS - SALIOU SAMB

Sai dai bayan gabatar mata da bukatun neman karin wa’adin da Burkina Fason da Guinea suka yi, kungiyar raya kasashen na yammacin Afirka ta ce za ta aike da tawaga zuwa kasashen biyu, gami da gudanar da taron koli kan halin da ake ciki.

A ranar Litinin ne sojojin Burkina Faso suka kawar da bukatar ECOWAS da ke neman su rage adadin shekaru 3 da suka dauka domin gudanar da gwamnatin rikon kwarya kafin mikawa farara hula mulki, domin a cewarsu abinda suka sanya a gaba shi ne murkushe ta’adancin da yayi sanadin mutuwar mutane kusan dubu da kuma raba wasu fiye da miliyan 1 da rabi da muhallansu.

A bangaren Guinea kuwa, mai magana da yawun gwamnatin kasar Ousmane Gaoual Diallo ya nanata cewar ba sa yin aiki a karkashin matsin lamba ko kuma umarnin kowa.

Zalika a lokacin da aka tambaye shi ko Guinea za ta fice daga kungiyar ECOWAS, sai ya ce, komai ma zai iya faruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.