Isa ga babban shafi
ECOWAS -MALI

ECOWAS ta jaddada takunkuman da ta lafta wa Mali

Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO ta jaddada takunkuman da ta lafta wa gwamnatin mulkin sojin Mali bisa jinkirta mayar da mulki ga hannun farar hula da ta yi.

Jean-Claude Kassi Brou, shugaba hukumar ECOWAS.
Jean-Claude Kassi Brou, shugaba hukumar ECOWAS. REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

A karshen taron da ta yi Ghana, ECOWAS ta kuma yi kashedi ga sojojin da suka karbe mulki a Guinea da Burkina Faso.

ECOWAS ta bukaci jagororin gwamnatin sojin Guinea da su gabatar da jadawali karbabe na mika mulki ga fara hula a karshen watan Afrilu, ko kuma su fuskanci takunkumai.

A wata sanarwa, ECOWAS din ta ja kunnen sojojin da ke mulkin Burkina Faso da cewa idan ba su saki tsohon shugaba Roch Marc Christian Kabore da suka wa daurin talala ba zuwa Alhamis na mako mai zuwa, za a kakaba musu takunkumi.

Taron  da aka yi a birnin Accra na Ghana na zuwa ne watanni 3 bayan da kungiyar ta ECOWAS ta kakaba wa Mali takunkumai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.