Isa ga babban shafi
Mali

An gaza cimma matsaya a tattaunawar sojojin Mali da ECOWAS

Wakilin kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ya bar kasar Mali a jiya Juma'a, ba tare da cimma matsaya kan maida kasar ga mulkin farar hula ba, yayin wata tattaunawa da gwamnatin mulkin sojin kasar.

Goodluck Jonathan, tsohon shugaban Najeriya kuma wakilin kungiyar ECOWAS a tattaunawa da gwamnatin sojojin Mali.
Goodluck Jonathan, tsohon shugaban Najeriya kuma wakilin kungiyar ECOWAS a tattaunawa da gwamnatin sojojin Mali. REUTERS - AMADOU KEITA
Talla

A jiya Juma’a ne dai tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, da ke wakiltar kasashe 15 na kungiyar ECOWAS, ya sauka a Mali inda ya gana da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake matsin lamba ga sojojin da ke mulkin kasar da suka kwace mulki a shekarar 2020, wadanda a yanzu ake neman su sanya ranar gudanar da zabe a Mali.

Wani jami'in diflomasiyyar ECOWAS, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce tawagarsu ta bar Mali ne ba tare da jadawalin zabe ba.

Jami'in diflomasiyyar ya kara da cewa wakilan kungiyar kasashen yammacin Afirka za su koma kasar Mali nan da makonni, domin ci gaba da tattaunawa.

Gwamnatin sojan kasar Mali na cigaba da bijirewa matsin lamba daga kasashen duniya kan gaggauta maida mulki ga hannun farar hula, tare da yin watsi da alkawarin da aka yi tun farko na gudanar da zabe nan da karshen watan Fabrairun shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.