Isa ga babban shafi

Sai mun yi shekaru uku kafin mu mika mulki - Sojin Burkina Faso

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta ce za ta share tsawon shekaru 3 kan karaga kafin ta iya mika mulkin kasar a hannun zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya a kasar.

Sojin da ke mulki a Burkina Faso
Sojin da ke mulki a Burkina Faso © OLYMPIA DE MAISMONT/AFP
Talla

Ita dai kungiyar Ecowas/Cedeao ta bai wa sojoji a Burkina Faso da takwarorinsu na Guinea Conakry wa’adin zuwa jiya Litinin da su gabatar ma ta da sabon jawalin da ke fayyace ranakun da za su shirya zabuka a kasashensu, ko kuma su fuskanci sabbin takunkumai.

Da alama dai kasashen biyu dake yammacin Afirka ba za su kaucewa karin tukunkuman na kungiyar raya kasashen yankin wato Ecowas ba, la’akari da cewa ko a maraicen jiya, gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea ta nuna alamun yiwuwar twaite shirin na komawa mulkin farar hula.

Babu dai wata sanarwa daga shugabannin sojojin Burkina Faso da ita ma ke da wa'adin na litinin don gabatar da gamshesshen jadawalin na mika mulki ga farar hula bayan juyin mulkin da suka yi a watan Janairu.

Tun cikin watan Agustan shekarar 2020 ne kasashen uku yammacin Afirka suka fuskanci juyin mulki, har sau biyu a Mali daya a Guinea sai kuma daya a Burkina Faso.

Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS a watan da ya gabata sun shaidawa gwamnatocin sojan kasashen Guinea da Burkina Faso zuwa ranar 25 ga watan Afrilu da su bayyana yadda da kuma lokacin da za su mika mulki ga farar hula ko kuma su fuskanci takunkumi nan take.

Sai dai Kungiyar ECOWAS ba ta bayyana wane lokaci ko irin takunkuman da zata kakabawa Burkina Faso da Guinea ba, bayan cikar wa'adin ranar 25 ga watan Afrilu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.