Isa ga babban shafi

Ministan shari'a ya gurfana gaban kotu kan amfani da matsayinsa wajen daukar fansa

Lauyoyin Ministan Shari’ar Faransa sun ce an umurce shi da ya gurfana a gaban kotu domin fuskantar tuhumar amfani da matsayinsa ta hanyar da ba ta dace ba, abinda ya zama abin kunya ga gwamnatin shugaba Emmanuel Macron.

Ministan shari'ar Faransa Eric Dupond-Moretti.
Ministan shari'ar Faransa Eric Dupond-Moretti. AP - Christophe Ena
Talla

Sai dai lauyoyin sun ce nan take suka shigar da kara domin hana daukar matakin gurfanar da maigidan nasu.

Eric Dupond-Moretti, tsohon lauyan da yayi fice akan aikinsa kafin rike mukamin minista, tun a shekarar bara yake fuskantar tuhumar yin amfani da matsayinsa wajen daukar fansa kan abokan hamayyarsa a aikinsu na shari'a.

Eric Dupond ya zama ministan shari'a na farko a Faransa da aka tuhume shi a wani bincike na shari'a.

Zargin dai ya na da alaka da binciken da ake yi wa wasu alkalai uku, wadanda suka umurci ‘yan sanda a shekara ta 2014 da su nadi bayanan wayar tarho na lauyoyi da alkalai da dama da suka hada da Dupond-Moretti, a wani bangare na binciken tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy.

Sai dai ministan shari’ar ya musanta zargin, yana mai cewa yana yin aiki ne kawai da shawarwarin da ma’aikatansa suka bayar na gudanar da bincike kan kuskuren da alkalai da suka sa ido kan kwace bayanan wayar suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.