Isa ga babban shafi
FARANSA - iran

Macron ya yi kira ga Iran da ta saki mai binciken da ta daure

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira da a gaggauta sakin wata mai bincike Bafaranshiya ‘yar kasar Iran, da ke tsare a kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Geoffroy van der Hasselt Pool/AFP/Archivos
Talla

Cikin wata sanarwa fadar gwamnatin Faransa tace shugaba Macron ya yi wannan kira ne a wata tattaunawa mai tsawo ta wayar tarho da yayi ranar Asabar da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi.

Tun cikin watan Yunin shekarar 20219 hukumomin Iran ke tsare da Fariba Adelkhah, 'yar kimanin shekaru 62 kuma masaniya a fannin ilimin halayyar dan adam, wanda a mayar da ita gidan yari a farkon wannan watan, bayan yanke mata hukunci daurin shekaru biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.