Faransa tace akwai alamun samun nasara a tattaunawar nukiliyar Iran
Kasar Faransa tace akwai alamar samun nasara a tattaunawar da ake yi a Vienna domin warware takaddama akan shirin nukiliyar Iran.
Wallafawa ranar:
Wani jami’i a fadar shugaban Faransa yace duk da yake akwai batutuwa masu nauyi da ba’a kaima cimma yarjejeniya akai ba dangane da cirewa kasar Iran takunkumi, akwai alamar dake nuna haske dangane da taron dake gudana.
Jami’in yace shugaban Faransa Emmanuel Macron a cikin kwanaki masu zuwa zai tattauna da takwaran sa na Iran Ebrahim Raisi ta waya dangane da tattaunawar da ake gudanarwa.
Wadannan kalamai sun sha ban ban da wadanda ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le drian yayi a makon jiya, inda yake korafi akan tsaikon da ake samu wajen tattaunawar. Jagoran kungiyar kasashen Turai wajen tattaunawar Enrique Mora yace an dakatar da tattaunawar yau juma’a domin bada damar daukar wasu matakai kafin ci gaba a makon gobe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu