Isa ga babban shafi
Faransa - Iran

Faransa ta yi tir da daurin shekaru 8 da aka yanke wa wani Bafaranshe a Iran

Faransa ta yi tirr da hukuncin dauri na tsawon shekaru takwas da wata Kotun Iran ta yankewa Benjamin Briere wani Bafaranshe, bisa samunsa da laifin leken asiri.

Benjamin Briere, bafaranshen da Iran ta daure bisa laifin leken asiri.
Benjamin Briere, bafaranshen da Iran ta daure bisa laifin leken asiri. - Saeid Dehghan's Twitter account/AFP/File
Talla

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar ta ce, ta ce ba za ta amince da hukuncin daurin ba, domin kuwa an cafke Briere ne a yayin da yayi balaguro a matsayin dan yawon bude ido zuwa kasar ta Iran.

Benjamin Briere, mai shekaru 36, shi ne fursuna tilo na yammacin Turai da a halin yanzu yake tsare a Iran wanda ba shi da fasfon kasar, wanda kotun ta kara laftawa wani hukuncin daurin na dabam na tsawon watanni takwas bisa laifin yada farfaganda kan tsarin Musulunci na Iran.

Briere, wanda ke tsare a gidan yarin Vakilabad da ke gabashin birnin Mashhad, an kama shi ne a watan Mayun shekarar 2020, bayan da ya dauki hotuna a wani wurin shakatawa ta hanyar amfani da wani jirgi mara matuki na nishadi, a halin yanzu kuma yana yajin cin abinci.

Bafaranshen na daya daga cikin 'yan kasashen yammacin Turai fiye da goma da ake tsare da su, matakin da masu fafutuka suka bayyana a matsayin garkuwa da su, domin kuwa ba su da wani laifi.

Hukuncin da aka yanke wa Briere na zuwa ne a daidai lokacin da Iran da manyan kasashen duniya ke neman cimma matsaya a tattaunawar da ake yi a Vienna kan batun farfado da yarjejeniyar 2015 kan shirin nukiliyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.