Isa ga babban shafi

Ana zargin Macron da kulla alakar sirri da kamfanin Uber

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na fuskantar matsin lamba kan neman ya fayyace gaskiyar abinda ya faru, dangane da zargin da ake masa na goyon bayan da ya baiwa kamfanin motocin haya na Uber, a lokacin da yake ministan tattalin arziki, kamar yadda wani rahoton fallasa ya bankado.

Emmanuel Macron.
Emmanuel Macron. © Susan Walsh / AP
Talla

Binciken da wasu kafafen yada labarai suka yi cikinsu har da jaridar ‘Le Monde’ ta Faransa da kuma ‘The Guardian’ na Birtaniya sun ce Macron ya gudanar da wasu tarurruka da ba a bayyana ba tare da shugabannin kamfanin Uber yayin da yake rike da mukamin minista daga shekarar 2014-2016.

Da take ambaton wasu takardu da sakwannin sirri na boye da suka bayyana, jaridar Le Monde ta yi zargin cewa shugabannin Uber sun kulla wata yarjejeniya a asirce da Macron a game da shirin kayyade ayyukan kamfanin nasu a daidai lokacin suke kokarin  bunkasa kasuwar hayar motocinsu na tasi.

Alamar kamfanin sufurin motocin haya na Uber.
Alamar kamfanin sufurin motocin haya na Uber. REUTERS - Mike Blake

Rahoton bankadar ya kara da cewa a karkashin yarjejeniya sirrin akwai alkawarin cewa Macron, wanda ke a matsayin ministan kudi a waccan lokacin ya yi alkawarin taimakawa Uber domin tabbatar da ya amfana da dokokin sa ido kan sufurinsa da aka gabatar a shekarar 2014.

Wani dan majalisa mai ra'ayin rikau Alexis Corbiere na jam'iyyar Unbowed ya ba da shawarar ‘yan majalisar Faransa su gudanar da bincike kan lamarin, wanda zai iya zama abin kunya ga shugaba Macron mai shekaru 44 da ya rasa rinjaye a majalisar dokokin kasar a zaben watan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.