Isa ga babban shafi
Rasha-Majalisar Dinkin Duniya

Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya zai ziyarci Rasha mako mai zuwa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres zai kai ziyara cikin mako a Rasha tare da ganawa da shugaba Vladimir Putin kamar dai yadda wata sanarwa daga Fadar Kremlin ta sanar.

Antonio Guterres, magatakardar majalisar dinkiin duniya.
Antonio Guterres, magatakardar majalisar dinkiin duniya. AP - John Minchillo
Talla

Ziyarar wanda zai fara ranar 26 ga wannan wata, Antonio Guterres, bayan isar shi a birnin Moscow zai fara tattaunawa ne da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov kafin daga bisani ya gana da shugaba Putin kamar dai yadda mai magana da yawun fadar ta Kremlin Dmitri Peskov ya tabbatar.

Tun ranar talatar da ta gabata ne Guterres ya tura wa shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky wasiku don sanar da su cewa zai ziyarci kasashen biyu da yanzu haka ke fada da juna.

Tun farkon barkewar wannan rikici a ranar 24 ga watan fabarairu, ana iya cewa an mayar da MDD share dayaba tare ba ta damar taka rawar da ta dace don warware wannan rikici ba, kuma an samu wannan tseko ne sakamakon bambancin ra’ayoyi a tsakanin manyan kasashe masu kujerun dindindin a majalisar.

Ziyarar ta makon gobe, za ta kasance wata babbar dama ga Mr Guterres, domin tattaunawa da nufin samar da maslaha a wannan rikici da za a iya cewa ya shafi duniya  baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.