Isa ga babban shafi
Amurka-Katolika

Majami'ar Katolika za ta biya diyyar Dala miliyan 87 kan cin zarafi

Majami'ar Katolika da ke Amurka ta ce reshenta da ke New Jersey ta amince ta biya diyyar Dala miliyan 87 da rabi ga mutanen da aka ci zarafin su a karkashin cocin.

An samu rahotannin cin zarafin yara a majami'un Katolika a sassan Turai, matsalar da hukumomin majami'ar ke kokarin warwarewa.
An samu rahotannin cin zarafin yara a majami'un Katolika a sassan Turai, matsalar da hukumomin majami'ar ke kokarin warwarewa. © AP/Czarek Sokolowski
Talla

Sanarwar ta biyo bayan kulla yarjejeniya tsakanin mujami’ar Camden da ke kusa da Philadelphia da wakilan mutane 300 da limaman cocin suka ci zarafin su ta hanyar lalata tsakanin shekarar 1970 zuwa 1980.

Wannan adadi ya zarce na Dala miliyan 85 da mujami’ar Boston ta biya a shekarar 2003 amma bai kai wadanda aka biya a mujami’un California da Oregon ba.

Kafar sadarwar bishop-accountability.org ya ce sau 4 kacal aka biya kudin da ya zarce Dala miliyan 100 a matsayin diyya tun daga shekara ta 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.