Isa ga babban shafi
Faransa-Katolika

Majami'ar Katolika za ta sayar da kadarori don biyan diyyar yaran da aka lalata

Majami'ar Katolika da ke Faransa ta sanar da shirin fara sayar da wasu kadarorin ta domin biyan diyya ga mutanen da limaman cocin suka ci zarafinsun ta hanyar lalata galibi kananan yara.

Wasu Limaman majami'ar Katolika a Faransa.
Wasu Limaman majami'ar Katolika a Faransa. REUTERS/Oswaldo Rivas
Talla

Sanarwar da taron shugabannin majami’ar suka sanar ta ce cocin zai sayar da kadarorin gidajen sa ko kuma karbar bashi domin biyan dubban mutanen da aka ci zarafin su lokacin suna yara kanana.

Shugabannin majami’ar na ci gaba da fuskantar karin matsin lamba daga bangarori da dama wajen ganin sun biya diyyar sakamakon wani bincike mai zaman kan sa da ya bankado yadda akayi ta samun cin zarafin yaran tsakanin shekarar 1950 zuwa shekara ta 2020.

Tun farko wani rahotan kwamitin bincike mai zaman kansa ne ya bankado yadda aka ci zarafin kananan yaran dubu 216 adadin da ya karu zuwa yara dubu 330 daga bisani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.