Isa ga babban shafi
Canada

Cocin Katolika ya nemi afuwa kan cin zarafin kabilu 'yan asalin Canada

Cocin Katolika ya nemi afuwar kabilu 'yan asalin kasar Canada, dangane da cin zarafinsu da limaman mujami’unsa suka shafe tsawon lokaci suna yi a makarantun da suka kafa tare da hadin gwiwar gwamnati don horas da yara bisa koyarwar ta darikar ta Katolika.

Wasu mutane yayin kallon tsohuwar Makarantar Kamloops inda aka bar furanni da katuna a watan Yuni na shekarar 2021, a zaman wani abin tunawa da yaran da aka gano an binne su kusa da ginin.
Wasu mutane yayin kallon tsohuwar Makarantar Kamloops inda aka bar furanni da katuna a watan Yuni na shekarar 2021, a zaman wani abin tunawa da yaran da aka gano an binne su kusa da ginin. © Cole BURSTON AFP/File
Talla

Matakin neman afuwar a ranar Juma’a, ya biyo bayan sakamakon binciken da aka samu kwanan nan wanda ya girgiza Canada, na gano wasu kaburbura dubu 1 da 200 marasa alama, da aka yi ittifakin na yara ne 'yan asalin kasar da aka tilastawa shiga makarantun na Katolika daga karshen shekarun dubu 1800 zuwa cikin 1990.

Bincike dai ya nuna cewar shugabannin makarantun da kuma malamansu, sun ci zarafin daliban ta hanyar duka da kuma fyade da zummar raba su da al’adunsu da kuma da yarensu.

Neman gafarar babban Cocin na Katolika dai na zuwa ne, kasa da mako guda, kafin bikin ranar Gaskiya da Sasantawa da aka ayyana a ranar 30 ga watan Satumba, don girmama 'yan asalin kasar Canada da suka bace, da kuma wadanda suka tsira daga makarantun da aka azabtar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.