Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Macron da Le Pen za su yi muhawara mai zafi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar takararsa Marine Le Pen sun yi musayar zafafan kalamai a yau Litinin, a dadai lokacin da suke komawa fagen yakin neman zabe gabanin fafatawarsu a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

Marine Le Pen da Emmanuel Macron
Marine Le Pen da Emmanuel Macron © REUTERS/Sarah Meyssonnier/Benoît Tessier/Montage RFI
Talla

Musayar zafafan kalaman na zuwa ne gabanin muhawarar da ‘yan takarar biyu za su yi wadda ake sa ran za ta fayyace ainihin wanda ya cancaci ya lashe zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

‘Yan takarar biyu sun gudanar da kwarya-kwaryar gangami a yayin bikin Easter, suna rige-rigen tallata kansu gabanin muhawararsu ta keke da keke da za su yi a ranar Laraba mai zuwa.

A yayin wannan muhawara, ana sa ran shugaba Emmanuel Macron mai ra’ayin ‘yan tsaka-tsaki ya kare salon mulkinsa na tsawon shekaru biyar a gaban Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayi.

Tarihi zai maimata kansa a bana, ganin cewa a shekara ta 2017, shugaba Macron ne da Le Pen suka fafata da juna a zagaye na biyu na zaben a wancan lokaci.

A karo na uku kenan da Le Pen ke neman darewa kujerar shugabancin Faransa, yayin da a bana take jaddada cewa, tana cikin kyakkyawan shiri fiye da sauran lokuta a baya.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, shugaba Macron na kan gaba a yiwuwar samun nasara a zaben fiye da Le Pen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.