Fiye da 'yan kasar Ukraine miliyan 4.4 sun tsere daga yaƙi: MDD
Majalisar Dinkin Duniya tace, fiye da 'yan gudun hijirar Ukraine miliyan 4 da dubu 400 ne suka tsere daga kasarsu tun lokacin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya fara kai musu hari a ranar 24 ga watan Fabrairu.
Wallafawa ranar:
Alkaluman Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar ya nuna cewa yanzu haka mutane miliyan 4 da 441,663 suka tsarewa Ukraine.
Hukumar tace, wannan shine adadi mafi yaw ana ‘yan gudun hijara da aka taba gani tun bayan yankin duniya na biyu.
Kashi 90 cikin 100 na wadanda suka tsere daga Ukraine mata ne da yara kanana, saboda hukumomin Ukraine ba sa barin mazan da suka kai shekarun aikin soji su fice.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu