Mutanen 50 sun mutu a harin da aka kaiwa tashar jiragen kasan Ukraine
Akalla mutane 50 da suka hada da kananan yara biyar ne suka mutu a wani hari da aka kai kan tashar jirgin kasa da ke birnin Kramatorsk a gabashin Ukraine.
Wallafawa ranar:
Gwamnan yankin Donetsk Pavlo Kyrylenko, ya tabbatar da alkaluman a shafinsa na Telegram, inda ya dora alhakin kai harin kan sojojin Rasha.
Kyrylenko ya yi gargadin cewa akwai yiyuwar adadin wadanda harin ya rutsa da su zai karu, yana mai cewa har yanzu akwai mutane 98 da suka samu raunuka ciki har da yara 16.
Gwamnan ya ce 12 daga cikin wadanda tashin hankalin ya shafa sun mutu ne a asibiti sakamakon raunukan da suka samu, yayin da aka kashe 38 a nan take.
An dai kai hari kan tashar jirgin kasan da ke Kramatorsk ne da safiyar ranar Juma'a, lokacin da daruruwan mutane suka taru, suna jiran a kwashe su daga gabashin Ukraine inda Rasha ta sabunta kaiwa farmaki.
Sai dai Rasha ta musanta kai harin, wanda ta zargi Ukraine da kaiwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu