Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

IEA na fargabar rikicin Rasha da Ukraine ya kawo cikas ga yaki da sauyin yanayi

Hukumar kula da makamashi ta duniya ta bayyana fargabar cewar yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine na iya yiwa yaki da sauyin yanayi zagon kasa.

Hukumar kula da makamashi ta duniya ta bayyana fargabar cewar yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine na iya yiwa yaki da sauyin yanayi zagon kasa.
Hukumar kula da makamashi ta duniya ta bayyana fargabar cewar yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine na iya yiwa yaki da sauyin yanayi zagon kasa. dpa/AFP/File
Talla

Babban daraktan hukumar kula da makamashin ta duniya Fatih Birol ya bayyana muhimmancin ganin gwamnatoci sun kara kaimi wajen cimma muradun yaki da sauyin yanayin, lokacin da yake bude taron majalisar ministocin makamashi na duniya a birnin Paris.

Birol yace yana cikin damuwa dangane da barazanar da yaki da sauyin yanayin ke fuskanta saboda yakin dake gudana a Ukraine.

Hukumar a cikin wannan wata ta bayyana cewar an samu Karin kashi 6 na sinadarin dake gurbata muhalli a shekarar da ta gabata wanda ya kai sama da tan 36 a daidai lokacin da tattalin arzikin kasashen duniya ke farfadowa sakamakon annobar korona.

Suma kasashen Yammacin duniya na cike da damuwa dangane da samun makamashin tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.