Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

MDD ta soki shugabannin duniya saboda sauyin yanayi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki manyan kasashen duniya, inda ya ce sun aikata babban laifi saboda yadda suka yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu. Kalamansa na zuwa ne bayan fitar da wani sabon rahoto kan illolin sauyin yanayi, inda ya zargi manyan kasashen da ta’azzara matsalar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres AP - John Minchillo
Talla

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce, babban abin tashin hankalin da wannan sabon rahoton kwararrun ya kunsa, shi ne yadda matsalar ta sauyin yanayi ta yi wa rayuwar bil’adama illa.

Rahoton ya kuma bukaci tuhumar wadannan manyan kasashe na duniya saboda yadda suka gaza wajen daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar.

Mista Guterres ya bayyana cewa, kusan rabin al’ummar duniya na rayuwa cikin gagarumar barazana a yanzu, yayin da sukurkucewar alaka tsakanin halittu da muhalli ta kai matakin kololuwa a cewarsa.

Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, babu yadda za a karyata batun cewa, lallai hayaki mai gurbata muhalli shi ne ummul-haba-i-sin sauyin yanayin.

Sannan ya ce, watsi da nauyin da ya rataya akan shugabannni na matsayin babban laifi, kuma manyan kasashen duniyar da suka fi gurbata muhalliu, su ne da laifin cin amanar  doran duniyar da muke rayuwa a ciki a cewarsa.

An dai fitar da rahoton kwararrun ne na Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da rikcin Rasha da Ukraine ke daukar hanklulan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.