Isa ga babban shafi
Ukraine - Rasha

Sama da mutane miliyan 10 sun tsere daga mamayar Rasha a Ukraine- MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace yanzu haka adadin mutanen da suka kauracewa gidajensu a Ukraine domin neman faka ya haura miliyan 10 wato fiye da kashi ɗaya bisa huɗu na al'ummar ƙasar saboda "mummunan yaƙi" da  Rasha da kaddamar a kasar.

Wasu 'yan kasar Ukraine dake tsarewa rikicin kasar zuwa Poland, 27/02/22.
Wasu 'yan kasar Ukraine dake tsarewa rikicin kasar zuwa Poland, 27/02/22. © AP/Visar Kryeziu
Talla

Shugaban Hukukumar Kula da ‘yan gudun Hijara ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR Filippo Grandi yace daya daga cikin nauyin da ke rataya a wuyan wadanda ke haifar da yaki ko'ina a fadin bala’in da ake gefa fararen hula ciki wato tilasta musu barin gidajensu,"

Wasu 'yan kasar Ukraine dake tsarewa rikicin kasar zuwa kasashe makwabta.
Wasu 'yan kasar Ukraine dake tsarewa rikicin kasar zuwa kasashe makwabta. AP - Sergei Grits

"Yakin da ake yi a Ukraine yana da muni sosai, wanda ya sa mutane miliyan 10 suka yi gudun hijira ko dai a cikin kasar, ko kuma a matsayin 'yan gudun hijira a kasashen waje."

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, tace ‘yan kasar Ukraine 3,389,044 ne suka bar kasar tun bayan fara mamayar Rasha a ranar 24 ga watan Fabrairu, yayin da wasu 60,352 suka bi sahu tun daga ranar Asabar da ta gabata.

Kusan kashi 90 cikin 100 na wadanda suka gudu mata ne da kananan yara, saboda Mazajen a Ukraine masu shekaru 18 zuwa 60 sun cancanci shiga kiranyen soji kuma ba za su iya barin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.