Isa ga babban shafi
RASHA-UKRAINE

Rasha na fuskantar suka da takunkuman karya tattalin arziki kan Ukraine

Manyan kasashen yammacin duniya na gaggawar mayar da martani ga matakin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya dauka na amincewa da 'yancin cin gashin kan wasu yankuna biyu na ‘yan tawaye dake gabashin Ukraine da kuma tura sojoji yankin, yayin da Amurka da kasashen Turai ke shirin sanya mata takunkumai.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin lokacin da yake sanya hannu don amincewa da wasu yankunan Ukraine biyu amatsayin masu gashin kai.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin lokacin da yake sanya hannu don amincewa da wasu yankunan Ukraine biyu amatsayin masu gashin kai. Alexey NIKOLSKY Sputnik/AFP
Talla

Wannan mataki ya sa tuni Jamus ta sanar da dakatar gagarumin aikin gina bututun iskar gas na Nord Stream 2 daga Rasha, ta kuma ce Tarayyar Turai za ta dauki tsatsauran mataki na takunkumin tattalin arziki.

Amurka

Fadar White House ta yi maraba da matakin da Jamus ta dauka kan bututun mai, ta kuma ce za ta bayyana nata matakan nan bada dadewa ba, yayin da Birtaniya ta sanya takunkumi kan bankunan kasar Rasha biyar da kuma wasu attajiranta uku.

Ukraine

A halin da ake ciki, Ukraine, ta kira babban jami'in diflomasiyyarta daga Moscow, a daidai lokacin da shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya yi gargadin cewa matakin Putin na amincewa da yankunan da suka balle, tamakar shirin mamayar soji ne ya fito karara.

Estonia

Shugaban kasar Estonia Alar Karis wanda yayi gaggawar zuwa Ukraine domin jajinta masa, yayi Allah wadai da matakin Rasha.

Faransa

Firaministan Faransa Jean Castex yace Rasha na keta dokokin kasa da kasa, yana mai cewa kasar za ta goyi bayan duk wani takunkumin da za’a kakabawa Rasha yayin da kuma za ta ci gaba da neman sulhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.