Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Rasha ta fayyace mutanen da za ta kashe - Amurka

Kasar Amurka ta yi gargadin cewa Rasha ta fara lissafa jerin sunayen mutanen da za ta hallaka da kuma wadanda za a aike da su gidajen yari da zarar ta yi nasarar mamaye Ukraine.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin © Alexei Nikolsky/AP
Talla

Amurkan na wadannan kalamai  ne ta cikin wasikar da ta aike wa shugaban Majalisar Dinkin Duniya daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da gargadin Rasha da kakkausar murya kan kada ta sake ta mamayi Ukraine din.

Wasikar da Amurkan ta aike na kunshe da bayanin cewa, abin fargabar shi ne yadda Rasha ta fara lissafa sunayen wasu fitattun mutane da za ta hallaka, da kuma wadanda zata daure a gidan yari bayan ta mamayi Ukraine din.

Amurkan ta ce, wannan hali da Rasha ta jefa Ukraine ya haifar da rashin tsaro da kuma tabarbarewar al’amurra da bude kofar aikata manyan laifuka irin su garkuwa da mutane da azabtar da su da fadan addini da na Kabilanci da sauran rikice-rikice a Ukraine din.

To amma dai tuni manyan kasashen duniya ke ci gaba da gargadin Rasha  kan kada ta kuskura ta mamaye Ukraine kawai don takalar fada da tono yaki, matukar ba haka ba kuma to tabbas zata dandana kudar ta.

Sai dai da alama ko a jikin Rasha game da wannan Gargadi la’akari da yadda take ci gaba da kai karin dakaru iyakar Ukraine da kuma basu damar kara matsar kasar da nufin jiran umarnin afka mata, duk da dai tana musanta zargin afkawa Ukraine din, tana mai cewa ta jibge dakarun ne kawai don baiwa kanta kariya.

Duk wannan dambarwa na zuwa ne a dai-dai lokacin da Ukraine ta musanta ikirarin Rasha na hallaka wasu dakarun kasar biyar, da ta yi zargin sun shiga Rasha ba bisa ka’ida ba da nufin yi mata leken asirin da cin dunduniyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.