Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Biden da Putin sun amince su tattauna idan Rasha ba ta mamaye Ukraine ba

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran sa na Amurka Joe Biden sun amince su gudanar da wani taro a tsakanin su muddin Rasha bata mamaye Ukraine ba domin rage tankiyar da ake samu da kuma kaucewa barkewar yaki.

Joe Biden da  Vladimir Putin sun amince su tattauna muddin Rasha ba ta mamaye Ukraine ba.
Joe Biden da Vladimir Putin sun amince su tattauna muddin Rasha ba ta mamaye Ukraine ba. Jim WATSON, Grigory DUKOR AFP/File
Talla

Kasar Faransa ce ta sanar da amincewar shugabanin kasashen Rasha da Amurka na ganawa a tsakanin su sakamakon shiga tsakanin da shugaba Emmanuel Macron yayi.

Wani babban jami’in gwamnatin Faransa yace bangarorin biyu ne zasu bayyana lokacin da za’ayi taron da kuma wurin gudanar da shi, yayin da ake saran ya kunshi masu ruwa da tsakaki akan rikicin Ukraine.

Wannan gagarumin ci gaba ya zo ne bayan da Amurka ta bayyana cewar, Rasha ta kammala duk wani shirin da ya kamata domin mamaye Ukraine, yayin da kasashen biyu suka zargi juna saboda musayar rokoki.

Rahotanni sun ce akalla mutane 500 suka shiga zanga zanga a Birnin Madrid dake Spain domin nuna rashin amincewar su da yunkurin mamaye Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.