Isa ga babban shafi

'Yan sandan Faransa sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da dokokin Korona

‘Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye, tare da cin tarar daruruwan mutane a jiya Asabar don tarwatsa ayarin motocin da suka yi yunkurin datse hanya a wata zanga zangar  adawa da dokokin da hukumomi suka kakaba don dakile cutar Covid-19 da kuma tsadar rayuwa da suke fuskanta.

Hayaki mai sa hawaye da 'yan sanda suka harba  wa masu zanga-zanga a Paris.
Hayaki mai sa hawaye da 'yan sanda suka harba wa masu zanga-zanga a Paris. AP - Adrienne Surprenant
Talla

Mutanen da suka samu  kwarin gwiwa daga abin da direbobin manyan motoci a babban birnin Canada, Ottawa suka yi, sun fito da dayawa daga sassa dabam dabam na Faransa don gudanar da wannan zanga zanga.

‘Yan sandan, wadanda suka haramta zanga zanga, sun yunkura cikin hanzari don taka wa masu kokarin shiga birnin Paris birki, inda suka ci tarar da dama da suka shiga haramtacciyar zanga zangar.

Sai dai fiye da ababen hawa 100 sun samu kai wa ga dandalin nan na Champs-Elysees, inda nan ne ‘yan sanda suka harba musu barkonon tsohuwa, abin da ke tuni da zanga zangar masu tufafin ruwan dorawa ta Yellow vex.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.