Isa ga babban shafi
Jamus - Siyasa

Olaf Scholz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus

'Yan majalisar dokokin Jamus sun zabi Olaf Scholz a matsayin sabon shugaban gwamnatin kasar, wanda ya kawo karshen mulkin 'yan mazan jiya na tsawon shekaru 16 karkashin Angela Merkel, kamar yadda zakuji cikin wannan rahoto da Ahmad Abba ya hada mana, sabon shugaban nada kalubale da dama.

Sabon shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, da mai barin gado Angela Merkel yayin bukin mika mulki,08/12/21.
Sabon shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, da mai barin gado Angela Merkel yayin bukin mika mulki,08/12/21. AP - Markus Schreiber
Talla

Olaf Scholz, wanda ya lashe zaben da kuri'u 395 daga cikin 707, zai jagoranci kawancen jam’iyyun SPD, da kuma FDP, kawancen da tuni ya sha rantsuwar kama aiki a wannan Laraba na fuskantar wasu manyan kalubale nan take, wanda suka hada da yaki da annobar korona, sauyin yanayi zuwa rikici da Rasha da China.

Annobar korona

Batun annobar korona da yanzu hake ke kara ta’azzara a Jamus ya kasance daya daga cikin manyan kalunale da sabon shugaban na gwamnatin Jamus ke fuskanta, wanda tun kafin rantsuwar kama aiki, sai aka tilasta masa daukar mataki.

Sabon shugaban gwamnatin daga jam'iyyar SPD Olaf Scholz da tawagarsa sun amince da sabbin takunkumi kan mutane da basu karbi allurar rigakafi ba, kuma tuni suka shirya sanya kafar wando guda da masu fatali da allurar, wajen shirin tilasta rigakafin cikin makonnin masu zuwa.

A yayin rantsar da sabuwar majalisar ministocin a wannan Laraba, Shugaba Frank-Walter Steinmeier ya bukaci Scholz da ya “tabbatar da cewa annobar ba ta yi tasari kan harkokin rayuwar al’umma ba.

Sauyin Yanayi

Sabuwar gamayyar dai na shirin zuba jari mai yawa wajen tinkarar sauyin yanayi, da nufin inganta makamashin da bai gurbata muhalli tare da  kawar da kwal nan da shekarar 2030.

Sun kuma amince da samar da motoci miliyan 15 masu amfani da wutar lantarki nan da shekarar ta 2030, sama da 500,000 da ake da su a halin yanzu.

Sai dai kuma jam'iyyun gamayyar sun yi alkawarin ba za su kara haraji da kuma neman bashi ba, lamarin da ya sa da dama ke tambayar daga ina kudaden za su fito.

An dakatar da dokar basussuka da ke cikin kundin tsarin mulkin Jamus bayan barkewar cutar korona, wanda ya baiwa gwamnati damar ciyo biliyoyin kudade don fitar da ita daga matsalar.

Turai

Jam'iyyun sun nuna sha’awar kara karfin ikon nahiyar Turai" -- mai yiyuwa ne su faranta wa kasa ta biyu mafi girma a nahiyar wato Faransa rai, wadda ta ba da fifiko ga shugabancinta na EU tun daga shekara ta 2022.

Scholz zai kai ziyarar birnin Paris, wanda zata kasance ta  farko ta kasa da kasa, ya kuma shaida wa manema labarai a Berlin cewa yana son ci gaba da kokarin Jamus na samar da "karfi, 'yancin kai da bude kofa ga Tarayyar Turai".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.