Isa ga babban shafi
Georgia - siyasa

Tsohon shugaban kasar Georgia ya kawo karshen yajin cin abinci na kwanaki 50

Shugaban 'yan adawar Georgia kuma tsohon shugaban kasar Mikheil Saakashvili da aka daure a gidan yari ya kawo karshen yajin cin abinci na kwanaki 50 da yake yi bayan da aka dauke shi zuwa asibitin sojoji daga asibitin kurkuku.

Masu zanga zangar neman sakin tsohon shugaban kasar Georgia dake tsare a kurkuku
Masu zanga zangar neman sakin tsohon shugaban kasar Georgia dake tsare a kurkuku © AP Photo/Zurab Tsertsvadze
Talla

Mai fafutukar neman sauyi na yammacin Turai ya fara yajin cin abinci bayan da aka daure shi bayan dawowar sa daga kasar Ukraine inda yake gudun hijira a ranar 1 ga watan Oktoba, yana cewa kamun nasa siyasa ne.

A ranar Alhamis, Saakashvili, mai shekaru 53, ya tsuma, kuma likitoci sun bukaci hukumomi da su kai shi asibitin dake wajen kukuru, suna mai cewa rayuwarsa na cikin hadari.

Da farko hukumomin Georgia sun yi watsi da shawarwarin likitocin, amma ministan shari'a Rati Bregadze ya ce a shirye suke don dauke Saakashvili zuwa asibitin sojoji "inda jihar za ta kare lafiyarsa da tsaronsa."

Da sanyin safiyar Asabar, an dauke Saakashvili "daga asibitin kurkukun zuwa asibitin sojoji" a birnin Gori, mai tazarar kilomita 90 daga yammacin babban birnin kasar Tbilisi, kamar yadda lauyansa Dito Sadzaglishvili ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.