Hukumomin Georgia sun tsare tsohon shugaban kasar Mikheil Saakashvili
Hukumomi a Georgia sun cafke tsohon shugaban kasar Mikheil Saakashvili ranar Juma'a jim kadan bayan dawowarsa daga gudun hijira, bayan da sukayi fito na fito da magoya bayansa a cikin 'yan adawa.
Wallafawa ranar:
Saakashvili, fitaccen mai fafutukar neman canji na Yammacin Turai wanda ya bar ƙasar a karshen wa'adin mulkin shugabancinsa na biyu a shekarar 2013, ya ba da sanarwar dawowar gida a wani saƙon bidiyo.
Abokan hamayyarsa a jam'iyyar Dream Party ta Georgia sun yi gargadin cewa za a kama shi kan zargin cin zarafin ofishinsa muddun ya koma gida, kuma Firanminista Irakli Garibashvili ya ce an hanzarta tsare shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu