Isa ga babban shafi
NATO

NATO ta bude cibiya a Georgia

Kungiyar Tsaro ta NATO ko OTAN ta bude wani sansanin bayar da horo a kasar Georgia da ke neman bunkasa dankon zumunci tsakaninta da kasashen Turai, duk da barazanar Rasha kan rikicin Ukraine.

Sakataren tsaron NATO Janar Jens Stoltenberg
Sakataren tsaron NATO Janar Jens Stoltenberg REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Georgia ta sami ‘yancin kanta ne daga kasar Rasha da ke zaman doya da manja da kasashen Turai.

Georgia ta dade tana neman shiga kungiyar kasashen NATO, kuma yanzu haka ana saran zuwa badi ta fara samun shiga cikin kungiyar a mataki na farko.

Wasu masana na ganin zai yi wuya Georgia ta sami shiga wannan kungiyar zuwa badi, don gudun kada Rasha ta kalli abin tamkar cin fuska, ta yadda rikicinta da Ukraine zai kara damewa.

Babban Sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg, bai yarda ya gaskata ko musanta zancen ba.

Bude sansanin horaswan da NATO ta yi a wajen garin Tbilisi na kasar Georgia, ana ganin an yi hakan ne domin kare kasar, wadda har yakin kwanaki biyar ta gwabza da Rasha a shekara ta 2008.

A cewar Babban Sakataren NATO, wanda ya halarci bude cibiyar, ya shaidawa manema labarai tare da mai masaukinsa Firaministan Georgia Irakli Garibashvili cewa za a rika horas da Dakarun NATO tare da na Georgia a cibiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.